Manufofin Mu

DANDALIN TALLAFAWA MATASA DA WANZAR DA ZAMAN LAFIYA DON CI GABAN KASAR MU NIGERIA

MANUFOFIN MU

An kafa wannan dandali domin tallafawa matasa da shawarwari na yadda zasu dogara da kansu,sannan su taimaki al’ummarsu da kasar su, haka kuma da tattaunawa tare da yan majalisar wannan dandali masu kwazo da basira don wanzar da zaman lafiya don ci gaban kasar mu Nigeria.

Wannan dandali ba’a kafa shi da wata manufa don cin zarafin wani ko wata ba, zagi ko shagube na wani ko wata ba, habaici ko bakar magana ga wani ko wata ba, haka kuma duk dan wannnan dandali ya sani cewar wannan dandali nashi ne, saboda haka za’a tattauna abubuwa akan abin da suka shafi matasa maza da mata, inganta rayuwarsu da tunano yadda zasu zama mutane na kwarai a kasa Nigeria.

Bugu da kari wannan dandali zai tattauna yadda zamu samar da zaman lafiya a Nigeria lungu da sako na kasa baki daya musanman anan arewacin Nigeria inda aka fi magana da yaren Hausa, a garuruwa kamar Kano, Kaduna, Bauchi, Gombe, Maiduguri, Yobe, Zaria, Jos, Adamawa, Sokoto,Zamfara,Kebbi,Taraba, Katsina, Jigawa, Minna, Abuja, Kogi,Benue, da Nassarawa.

Al’umma da kasa basa samun cigaba sai da zaman lafiya da kwanciyar hankali,saboda haka ya zama wajibi mu yan Nigeria matasa maza da mata mu tashi tsaye domin tabbatar da wanzuwar zaman lafiya a wannan kasa mai albarka da daraja a idon duniya wato Nigeria.

Taimaka da shawarwarin ka, sannan ka kasance kullum kana ziyartar wannan dandali domin bada taka gudunmawar na tabbatar da abubuwan da aka zayyana a sama.

Tabbatar kayi rijista da wannan dandali kuma ka tabbatar ka janyo hankalin matasa masu kishin kasa cikin wannan dandali don bada tasu gudun mawar.

DOKOKIN MU SUNE :

Babu maganar kwallon kafa ko fim ko siyasa ko hirar soyyayya da yan mata ko zagin shugabanni ko wata jinsin al’umma.

TUNTUBE MU KAI TSAYE

dandalintallafawamatasa@gmail.com

07037733303

Advertisements

Leave a Reply

Fill in your details below or click an icon to log in:

WordPress.com Logo

You are commenting using your WordPress.com account. Log Out /  Change )

Google+ photo

You are commenting using your Google+ account. Log Out /  Change )

Twitter picture

You are commenting using your Twitter account. Log Out /  Change )

Facebook photo

You are commenting using your Facebook account. Log Out /  Change )

Connecting to %s